Menene Zai Faru Da Harkar Internet Nan Gaba?

Ko Ƙaƙi Ko Kaso Nan Gaba Harkar Internet Da Computer Zata Karade Duniya Gabadaya, A Wancan Lokacin Duk Waɗanda Suka Riga Sukayi Gini Tun Yanzu Sune Zasu Kasance Ahead Of The Game, Sune Zasu Ringa Baiwa Na Baya Wajen Zama, Kamar Waɗanda Suka Gina Great Platforms, Softwares, Ko Products Masu Amfani.

Zuwa Wannan Lokacin Kowa Burinsa Shine Ya Gina Career Ɗinsa Ta Internet Daga Kan Ƴan Siyasa, Yan Kasuwa, Da Professionals Irinsu Doctors, Lawyers, Consultants Da Sauransu.

Zuwa Wannan Lokaci Duk Abinda Kuke Ganinsa Yau Da Arha Da Sauƙi, Samunsa A Banza To Nan Gaba Zai Zama Da Wahala, Watakila Sai Ka Biya Kuɗaɗe Kafin Ka Samu Dama.

Zuwa Wancan Lokacin Kamfanonin Internet (Irinsu Selidia, Temu, Simas Academy, Google, Amazon, Meta, Da Sauransu) Zasu Fi Na Zahiri Yawa Da Tasiri A Duniyar, Ai Tun Yanzu Mun Fara Gani, To Me Yasa Ba Zamu Tsaya In Position Ba?

Zuwa Wancan Lokacin Komai Da Komai Zaiyi Migrating Ya Koma Digital (Paperless, Wireless, Cashless), Wayoyin Da Muke Riƙewa A Hannun Mu Zasu Sauya Tsari.

Maganar Samun Kuɗi Kuwa Zai Kasance Idan Ba Solid Abu Kake Dashi Ba, Ba Lallai Ka Samu Kuɗi Ba, Sai Dai Ka Zama Consumer Ko Kuma Wanda Yake Bauta Ana Jefa Masa Taro Da Sisi. Sirrin Shine Tun Yanzu Ka Fara Gini, Ka Tara Users, Ka Tara Community, Kayi Musu Offering Ɗin Value. Value Asalin Value Wanda Nan Gaba Za'a Buƙace Shi Ba Outdated Stuffs Ba.

An If You're Into Investment, Kamar Forex, Crypto, Stocks Investment, Ko Direct Investor (More Profitable), Dole Ya Kasance Ka Lakanci Wasu Skills Da Sirrukan Da 80%+ Basu Sani Ba, Domin Gujewa Faɗawa SL Ko Loss Mai Gabadaya.

Zuwa Nan Gaba Techie Zai Zama Daga Cikin Mutane Masu Daraja A Duniya Ko Wanda Ya San Abinda Yake Yi Dangane Da Internet Da Fasaha, Domin Komai Yana Karkashin Sarrafawarsu.

Maganar AI Zai Shigo, Amma Zuwa Lokacin Da AI Zai Rikiɗa Ya Koma AGI (Wato Lokacin Da Tunaninsa Zai Daidaita Da Ɗan Adam) Abubuwa Zasu Sake Gudu. Wasu Skills Ɗin Zasu Zama Outdated, (Therefore Wasu Ventures Ɗin Ko Ince Kamfani Zasu Mutu).

Har A Je Lokacin Da AGI Ɗin Zai Sake Rikiɗa Ya Koma ASI (Artificial Super Intelligence) A Wannan Lokacin Na Sama (Ahead Of The Game) Sune Zasu Ci Karensu Babu Babbaka. Competition Zaiyi Wahala (Domin Za'a Samu Tycoons Da Yawa) Matuƙar Ba AI Ka Ɓullo Musu Ba, Yin Nasara Zai Baka Wahala. Shima Sai Ka Taso Da Ƙarfinka Da Masana ASI Masu Daraja.

(Duk Da Cewa Har Yanzu Suma Masana Da Masu Bincike Basu San Takamammen Lokacin Da AGI Zai Bayyana Ba Kafin ASI).

Nan Ina Magana Ne Nan Da Shekaru 20 Zuwa 50 Gaba, Amma Karka Ɗauka Babu Nisa, Yanzu Zamu Riski Wajen.

Allah Yasa Mu Dace, Mu Gama Lafiya.

Aliyu Saidu Jauro
21st May, 2026

Post a Comment

Previous Post Next Post