Labarin Wani Manomi Da Dokinsa Ya Bata

Wani Manomi Ne Dokinsa 🎠 Guda Ɗaya Ya Ɓata, Makwabtansa Suka Zo Suna Masa Jaje Suna Cewa, "Wannan Wane Irin Mummunan Abu Ne Ya Same Ka?"


Shi Kuma Sai Ya Ce Musu, "Watakila."

Washegari Dokin Ya Dawo Tare Da Wasu Dabbobin Daji A Tare, Makwabtan Suka Sake Zuwa Suna Taya Shi Murna Suna Cewa, "Wannan Wane Irin Alheri Ne, Gaskiya Kana Da Sa'a?"

Shi Kuma Sai Ya Sake Ce Musu, "Watakila."

Bayan Kwanaki Ɗansa Ya Samu Karaya Wajen Kokarin Baiwa Ɗaya Daga Cikin Dabbobin Abinci, Sai Makwabtan Suka Sake Kawo Masa Jaje Suna Cewa "Wannan Wane Irin Bala'i Ne?"

Shi Kuma Ya Sake Ce Musu, "Watakila."

A Wannan Labarin Zamu Fahimci Cewa Hankali Da Tunanin Dan Adam Yana Da Gazawar Fahimtar Gaskiyar Al'amarin Da Ke Faruwa A Daidai Lokacin Da Abin Yake Faruwa, Watakila Sai Bayan Abin Ya Gama Faruwa Zuwa Wani Lokaci.

​Wannan Shi Ne Ilimin Perspective (Wato Fuskar Da Mutum Yake Kallon Abubuwa), Wanda Ke Nuna Mana Cewa Ba Abin Da Ya Same Mu Ne Ke Kayyade Farin Cikinmu Ba, Face Ma'anar Da Muka Baiwa Abin Da Ya Same Mu.

Muna Yawan Gaggawar Danganta Al'amuran Da Suka Same Mu Suna Mara Kyau Ko "Mai Kyau" Ba Tare Da Mun Jira Mun Ga Inda Abin Zai Kare Ba, Wanda Hakan Ke Sa Mu Zama Bayin Yanayinmu.

Idan Ka Fahimci Yadda Zaka Kwantar Da Hankalinka Kuma Ka San Cewa Kowane Yanayi Guda Ne A Cikin Babban Labarin Rayuwarka, To Za Ka Samu Wani Irin Iko Na Musamman Da Rayuwar Ka.

Nasara Ita Ce Ikon Kasancewa Nitsasse, Tare Da Sanya Yakinin Cewa Kowane Kalubale Da Yazo A Rayuwarka, To Yana Ɗauke Ne Da Wani Boyayyen Nasara.

Saboda Haka Maimakon Ka Zauna Kayi Ta Zagi Kana Kushewa, Ka Kwamtar Da Kai Ka Lura Da Abubuwan Da Suke Faruwa, Me Take Koya Maka, Menene Yakamata Kayi Nan Gaba, Da Sauransu.

Allah Yasa Mu Dace.

Aliyu Saidu Jauro

📅 08, March 03, 2026

Post a Comment

Previous Post Next Post