Menene Ma'anar Pareto Principle Da Yadda Yake Aiki

Ko Ka San Menene Ma'anar Pareto Principle?


Wannan Ilimi Ne Dake Nuna Mana Cewa A Kusan Kowane Fanni Na Rayuwa, Akwai Wasu Kananan Ayyuka Masu Muhimmanci Wadanda Su Ne Ke Kawo Manyan Sakamako.

Mutane Da Yawa Zaka Tarar Suna Bata Lokacinsu Wajen Yin Ayyuka Da Dama Wadanda Ba Su Da Tasiri A Rayuwarsu, Suna Tunanin Cewa Yin Aiki Sosai Shi Ne Zai Kai Su Ga Nasara, Alhali Sirrin Nasara Yana Ga Gano Wadancan Kananan Ayyuka Guda Biyu Ko Uku Da Suke Da Karfin Sauya Yanayin Kasuwancinka Ko Rayuwarka.

Idan Kasan Yadda Zaka Mayar Da Hankalinka Ga Abubuwan Da Suke Da "Quality" Maimakon Abubuwan Da Suke Da "Quantity," Wato Yawa, Za Ka Ga Ka Samu Abinda Kake So A Cikin Kankanin Lokaci Ba Tare Da Ka Sha Wahala Ba.

​Wannan Tsarin Yana Da Tasiri Sosai A Fannin Digital Marketing Da Blogging, Inda Kadan Daga Cikin Rubutunka Ko Tallace-Tallacenka Suke Kawo Maka Mafi Yawancin Masu Karatu Ko Customers.

Saboda Haka, Madadin Tsaya Ka Rarraba Hankalinka A Wurare Da Dama, Ka Fara Gano Wadancan Customers Kashi 20 Ɗin Da Suka Fi Kawo Maka Mafi Yawan Riba, Ko Kuma Wadancan Halaye Guda 20 Da Suke Sa Ka Farin Ciki A Soyayya, Sannan Ka Zuba Karfinka A Kansu.

Nasara Ba Ta Ga Yawan Aiki, Kamar Ka Zama Aikatau, Nasara Tana Ga Hikimar Gano Inda Ya Dace Ka Sanya Karfinka Domin Samun Sakamakon Da Zai Ba Wa Kowa Mamaki.

📅 08 March 03, 2026

Post a Comment

Previous Post Next Post